Kotu ta haramtawa Le Pen shiga al'amuran siyasa a Faransa
March 31, 2025Kotun ta samu Le Pen da laifin almundahana da kudaden da aka ware domin gudanar da wasu muhimman ayyuka na musamman a EU, wanda hukuncin kotun ka iya haramta mata tsayawa takarar shugabancin kasar a zaben 2027 da kuma daurin akalla shekaru biyar a gidan yari.
Karin bayani: Faransa: Macron zai fafata da Le Pen a zagaye na biyu
Le Pen da ke shugabantar jam'iyyar masu ra'ayin rikau ta National Rally RN na kan gaba a sahun 'yan siyasar kasar da ka iya kasancewa zakaran gwajin dafi a zaben 2027.
Karin bayani: Macron da Le Pen sun zama zakarun Zaben Faransa
Matakin kotun ka iya kawo karshen burin Le Pen 'yar shekaru 56, damar kafa tarihi a kasar ta Faransa. Ta dai ki cewa uffan ga dandazon manema labarai a harabar kotun, duk da cewa ta zargi babban mai gabatar da karar da kokarin shafe tarihinta a siyasance.
Lauyanta ya sanar da manema labarai cewa Le Pen za ta daukaka kara domin kalubalantar hukuncin kotun.