Kotu ta aike da madugun adawar Turkiyya gidan yari
March 23, 2025Wata kotu a Turkiyya ta aike da magajin garin birnin Santanbul Ekrem Imamoglu, babban mai adawa da shugaban kasar gidan yari. Matakin kotun na wannan Lahadi na nufin dan siyasar zai zauna a gidan kaso har sai an kammala shari'ar da ake masa sabanin neman belin da lauyoyinsa suka bukata, wani abu da ake fargabar ka iya haddasa babbar zanga-zangarkin jinin gwamnatin Shugaba Recep Tayyip Erdogan da ba a ga irinta ba a cikin shekaru 10.
Fadar mulkin kasar da ke birnin Ankara ta musanta zargin katsalandan a shari'ar, tana mai cewa kotun na cin gashin kanta.
Jim kadan bayan aike wa da shi gidan kaso, 'yan jam'iyyar Imamoglu sun taru a wannan Lahadi, inda suka fara shirin zabar shi a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar CHP domin ya kalubalanci Shugaba Erdogan wanda ya kwashe shekaru 22 yana mulkin Turkiyya.