SiyasaAsiya
Kotu a Japan ta wanke 'dan shekara 89 da ke zaman wakafi
March 25, 2025Talla
Kotu a Japan ta bukaci bai wa mutumin da ya fi kowa dadewa a gidan yarin kasar Dala miliyan 1.4, sakamakon daure shi da aka yi bisa kuskure kan zargin kisa tun a wajen 1966.
Karin bayani: Hiroshima: Shekaru 78 da harin nukiliya
Iwao Hakamada ya shafe kimanin shekaru 60 a gidan yarin Japan yana jiran hukuncin kisa, duk da cewa 'yan uwansa da abokan arziki sun shafe tsawon lokacin suna ta fadi tashin ganin cewa an tabbatar da gaskiyar lamari da kuma adalci kan kazafin da aka yi wa masa.
Karin bayani: Azabtar da fursunoni a gidan yarin Makala
To sai dai lauyoyin da ke kare tsohon 'dan wasan damben "boxing" din sun nuna rashin gamsuwarsu kan kudin da kotun ta ce a biya Mr. Hakamada a matsayin diyya sakamakon ukubar da ya sha na tsawon shekaru.