Kotu a Finland ta tasa keyar dan Najeriya gidan kaso
September 1, 2025An sami Simon Ekpa mai shekaru 40 dan asalin Najeriya wanda kuma ke da shaidar zama dan kasar Finland da laifin baiwa kungiyoyi makamai da bama-bamai tare da tunzura wasu su aikata laifuka.
Kotun yankin Paijat-Home, ta ce shi ne jigo a kungiyoyi da ke fafutukar neman ‘yancin cin gashin kan yankin kudu maso gabashin Najeriya inda yakin basasa a tsakanin shekarun 1967-70 ya yi sanadin mutuwar dubban daruruwan mutane.
A cikin wata sanarwa da kotun ta fitar, ta ce ta samu Ekpa da laifi dumu-dumu gami da tunzura jama'a don aikata laifukan ta'addanci.
An kuma same shi da laifin zamba a haraji. Ekpa ya yi amfani da kafafen sada zumunta wajen samun wani matsayi a siyasance, kuma ya yi amfani da rudanin da aka samu a wata muhimmiyar fafutuka ta ‘yan IPOB a Najeriya da ya taka rawar gani a ciki, inji kotun.
Duk laifukan an aikata su ne a birnin Lahti na kasar Finland tsakanin shekarar 2021 zuwa 2024.