Koriya ta Arewa za ta kara taimakon Rasha kan yakin Ukraine
July 13, 2025Shugaba Kim Jong Un na Koriya ta Arewa ya tabbatarwa ministan harkokin wajen Rasha Seigei Lavrov cewa Pyongyang za ta ci gaba da goyon bayan Moscow kan yankin Ukraine, tare da karfafa gwiwar cewa nasarar na nan tafe.
Shugaban Kim Jong Un ya yi wannan furici ne a yayin ganawarsa da ministan harkokin wajen Rasha wanda yanzu haka kai ziyara a Koriya ta Kudu wadda zai karkare a yau Lahadi.
Kamfanin dillancin Koriya ta Arewa KCNA ya ambato Kim Jong Un na cewa a shiye kasarsa ta ke domin biyan daukacin bukatun Rasha ba tare da wani sharadi ba kan kudurin da take son cimma domin kawar da rikicinta da Ukraine tun daga tushe.
Koriya ta Arewa da Rasha dai sun kulla yarjejeniyar tsaro ta bai daya a tsakaninsu a shekarar bara, inda Pyongyang ta aike da dubban sojoji domin taimakawa dakarun Moscow da ke fagen daga a Ukraine tare kuma da tallafi na makamai masu linzami.