Najeriya da Nijar na kokarin kyautata hulda
March 13, 2025Ita dai wannan ganawa ta tsakanin jakadan Najeriya da ke zaune a Nijar Ambasada Mohammed Sani Usman, da ministan harkokin wajen kasar ta Nijar Bakary Yaou Sangaré, an yi ta ne da zimmar duba hanyoyin dawo da cikakkar hulda ta kasa da kasa tsanin kasashen biyu wanda kuma ganawar da wakilin na Najeriya ya yi za ta share fage na wata babbar tattaunawa da zata shafi kasashen biyu a nan gaba.
Sai dai kuma daga nata bangare ma'aikatar harkokin wajen Nijar ta fitar da 'yar karamar sanarwa a rubuce bayan tattaunawar, inda ta ce muhimman batutuwan da aka tattauna bayan batun da ya shafi zamantakewa, su ne batun tsaro a kan iyakokin kasashen biyu.
Da yake magana masanin harkokin tsaro da siyasa ta kasa da kasa farfesa Dicko Abdourahamane, ya ce ko da kan matsalar tsaro kadai Nijar da Najeriya ya kamata su zauna cikin tsanaki su fuskanci juna domin kasashe ne da suka raba iyakoki kimanin kilomita 1500 inda al'umomin kasashen biyu ke hulda a kulli yaumin da juna.
Abun jira a gani dai shi ne ba da jimawa ba a samu wata ganawa ta musamman tsakanin magabatan kasashen biyu na siyasa da ma na tsaro domin sake duba hulda tsakanin Najeriya da Nijar don ingantata ta yadda kowace kasa za ta ci moriyar wannan hulda ba tare da wani cikas ba.