Turai: Mafita kan kudin makamashi
September 13, 2022Talla
Ministocin makamashi na Kungiyar Tarayyar Turai za su halarci taron koli domin neman mafita daga barazanar da Rasha ke yi na katse wa nahiyar makamashin gas da ke ba Turai.
Ministan makamashin da kasuwanci na Jamhuriyar Chek da ke jan ragamar shugabancin karba-karba na kungiyar EU, ya bayyana cewa ya gayyaci daukacin takwarorinsa a ranar 30 ga watan Satumba a Bruxelles, da zummar dudanar da taron koli da zai duba matakan dauka game da matsalar ta makamashi.
Ministocin dai za su dora ne daga inda suka tsaya a farkon watan Satumba, wanda ya fara nazari kan tsadar wutar lantarki da gas da nahiyar ta ke fuskanta tun bayan soma yakin Ukraine.