Najeriya: Ya makomar tafiyar Tinubu/Shettima?
June 16, 2025Rikici ya barke ne, bayan da mahalarta taron sun zargi shugaban jami'yyar ta APC na kasa da kitsa manakisar cire Kashim Shettima a cikin takarar. Taron wanda aka gudanar a jihar Gombe, ya samu halartar dukkanin gwamnonin jami'iyyar da 'yan majalisun dokoki na kasa da ministoci da shugabannin jam'iyyar da manufar yin nazarin makomar APC da kuma tabbatar da goyon bayan Shettima da Tinubu a wa'adi na biyu.
Sai dai yadda Shugaban jam'iyyar na kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje da mataimakinsa a yankin Mustapha Salihu suka ki goyon bayan mataimakin shugaban kasa a wa'adi na biyu, ya sa aka tayar da yamutsi a taron. An dai bai wa hammata iska an kuma jefi shugabbanin da kujeru da robobi, inda aka tashi taron baram-baram. Jam'iyyar ta APC dai, na fatan sake tsayar da shugaban Najeriyar Bola Ahmed Tinubu a matsayin dan takararta a zaben 2027. Sai dai kuma abin tambayar shi ne, ko za a yi tafiyar ta 2027 da mataimakinsa na yanzu Kashim Shettima?