SiyasaTarayyar Rasha
Ukraine: Putin ya yaba da kokarin Trump
August 14, 2025Talla
Yabon Shugaba Vladimir Putin ga takwaransa na Amurka Donald Trump, ya zo ne yayin da shugabannin biyu ke shirin gudanar da wani taro mai muhimmanci tsakanin Amurka da Rasha a birnin Alaska a wannan Jumma'a.
A wata ganawa da ya yi da manyan jami'an gwamnati game da taron a yau, Putin ya fito a cikin wani gajeren bidiyo ne ya yi wannan yabo ga Donald Trump.
Shugaban na Rasha ya kuma nuna cewa za a iya cimma sharuddan zaman lafiya na dogon lokaci tsakanin kasashen da Turai, da ma duniya baki daya, idan aka samu yarjejeniya da Amurka kan ikon sarrafa makaman nukiliya.
A daya bangaren, shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskyy da sauran shugabannin Turai na aiki tukuru don tabbatar da an saurari ra'ayinsu yayin da Trump da Putin za su gana a goben.