Najeriya: Rantsar da shugaban kasa a majalisa
June 11, 2025Ita dai majalisar dokokin Najeriya ta 10 ta yi fice wajen dauko batutuwan da ke haifara da cece-kuce, kama daga yunkurin mayar da yin zabe ya zama dole da kuma hukunta duk wanda ya ci mutumcin taken Najeriya sai kuma wannan batu na amfani da doka domin sauya tarihin da aka daura dambarsa tun a shekara ta 1999 da aka sake kafa dimukurdiyya a kasar.
Tun daga wannan lokaci kawo yanzu ana rantasar da shugaban kasar ne a dandalin taro na kasa na Egale da ke birnin Abuja, wurin da ke bayar da dama ga dubban 'yan Najeriya su cire kwarkwatar idanuwansu yayin rantsar da shugaban da suka zaba. A yanzu majalisar dattawan na son canza wannan al'ada, har ma da gwama batun da sanya shugaban Najeriya ya rinka jawabi ga 'yan majalsar a duk ranar dimukurdiyya 12 ga watan Yuni. Tuni wannan mataki ya janyo mayar da martani a Najeriyar, musamman wadanda da su aka yi gwagwarmayar yanke cibiyar sake kafa dimukurdiyya a kasar.
Domin sauya batu na tarihi ga muhimmin al'amari muhimmi ne a Najeriyar, musamman danganta shi da ranar 12 ga watan Yuni da aka soke zaben da ake dangata shi da mafi sahihanci. Sabo dai akan ce tirken wawa, domin shekaru 26 kenan da sake kafa dimukurdiyya da ake rantsara da sabon shugaban Najeriya a dandalin Egale din da ke tsakiyara birnin duk bayan shekaru hudu. Majalisar dokokin Najeriyar dai kan gwada ta ga martanin 'yan kasar a kan wasu al'ammura, inda daga baya ta kan janye batun wanda shi ne damar da dimukurdiyya ta bai wa 'yan kasa.