Wa zai amfana da ganawar Trump da Putin?
August 14, 2025An ayyana wannan ganawa tsakanin Shugaba Donald Trump na Amurka da Shugaba Vladimir Putin jim kadan gabanin shirin tsagaita wuta da Ukraine ya kare, lokacin da shugaban na Amurka ya yi gargadin irin sakamakon da ke jiran Rasha muddun ta bijire wa shirin. Ganawar tana zuwa bayan manzon musamman na Amurka Steve Witkoff ya kai ziyara zuwa birnin Moscow na Rasha a farkon wannan wata na Agusta.
Babu tabbacin batutuwan da za a tattauna lokacin ganawar a Alaska da ke Amurka. Sai dai abin da ake da tabbas shi ne tattauna batun yakin da ke faruwa sakamakon kutsen da Rasha ta kaddamar kan kasar Ukraine. Duk da haka Amurka da Rasha sun kawar da Shugaba Volodymyr Zelensky na Ukraine daga cikin tattaunawar.
Mikhail Kasyanov tsohon firaministan Rasha daga shekara ta 2000 zuwa 2004 ga abin da yake cewa:
"Putin koyaushe yana taka-tsantsan da duk mutumin da yake rike da shugabancin Amurka, wanda ka iya tantance makomar duniya. Kuma duk abin da ya faru zai karade duniya."
Wannan ganawa za ta bai wa Shugaba Vladimir Putin na Rasha damar tattaunawa da daya daga cikin manyan shugabannin kasashen yammacin duniya, Shugaba Donald Trump na Amurka. Abin da masu adawa da yakin da Rasha ta kaddamar kan kasar Ukraine suke nuna adawa a kai, kamar yadda Dmitry Gudkov ya kasance dan siyasa na Rasha daga bangaren 'yan adawa ke cewa:
"Ga Putin samun damar ganawa da shugaban Amurka wata babbar dama ce a gare shi. Shi Trump abin da ya nuna shi ne amince da wannan yaki na aikata laifuka, tare da ba shi damar tattaunawa da shugabannin kasashen yammacin duniya."
Akwai kuma masu ganin Rasha tana cikin mawucin hali na tattalin arziki da ita kanta take neman hanyar kawo karshen wannan yaki da ke faruwa tsakanin kasar da Ukraine. Kirill Rogov masanin harkokin siyasa da ke shugabancin Sashen Rashanci na wata kafar yada labarai ta intanet, ga abin da yake cewa a kai:
"Putin kuma yana fata na saman karbuwa mai yuwuwa bisa zabi mafi tsauri maimakon ya jinkirta zuwa wani lokaci. Saboda zuwa karshen shekara, Putin zai shiga mawuyacin hali, idan hare-haren da Rashake yi suka ci gaba da rasa tasirin da ake bukata a fagen-daga, yayin da takunkumida aka kakaba wa Rasha ya janyo ta rasa Indiya a matsayin mai sayan kayayyakinta musamman mai."
Shi dai Trump ya dage da neman ganin samun zaman lafiya tsakanin Rasha da Ukraine, kuma zuwa yanzu ana samun kwan-gaba kwan-baya game da batun na samun zaman lafiya.