Ko kun san cewa harbin zuma na maganin cutuka?
July 16, 2025A kasar Kenya ana samun karuwar mutane masu imani da amannar harbin kudan zuma na kawo waraka ga cututtukan da ke damuwar mutane, inda mutane masu dauke da cututtuka ke kai ziyara a wata gona da aka tanadi kudan zuma da ke harbin masu cuta, a wani mataki na samun waraka.
Zumar da ake kiwo a gona da ake kira Bella farm Afrika, a garin Muranga da ke tsakiyar kasar Kenya, su ne suke janyo hankalin mutane musamman masu dauke da cututtuka irin su shanyewar rabin jiki, ko kuma wasu sassa na jikin mutum da ma karin wasu cututtuka da ke damun mutane, inda mutane ke zuwa ake kuma amfani dafin kudan zuma wajen samun waraka da dawowa da lafiya bayan ta kubuce.
Kudan zuman dai ana saka su ne ga sassa daban-daban na jikin marar lafiya sannan daga bisani a cire bayan sun harbi marar lafiya su kuma saki dafinsu, wanda kuma da shi ne aka yi amannar waraka ce ga marara lafiya a kasar ta Kenya.
Yanzu haka kwararru da masana masu bincike a wata cibiyar kasa da kasa da ke kula da kwari a Nairobi babban birnin kasar Kenya, na nazaratar dafin kudan zuma da kuma bayyana irin fa'idar da suke da shi.
Tuni dai mutane da dama 'yan kasar ta Kenya da ke fama da cutuka ke ta kokarin kai ziyara wannan gona domin samun waraka ga cututtukan.
A yanzu dai fatan da suke da shi wadanda suka kirkiri samar da warakar cututtuka ta hanyar kudan zuma, hukumomin kasar Kenyan su amince masu su samar da allurai da ake sarrafawa da dafin Kudan zumar da mutane za su iya saye.