Kauracewa cin nama da duk wani dangi na dabbobi ko tsuntsaye, wani nau'i ne na rayuwa da mutane ke yi domin radin kansu ba wai don dalilai na rashin lafiya ba. Wannan sabuwar dabi'a ce a kasashen Afirka, inda kalilan daga mutane ke zabar kin cin naman da duk wani abu da ya shafi dabbobi ko tusntsaye.