Najeriya: Mene ne mafitar siyasar 2027?
May 26, 2025Wakilai daga daukacin jihohin yankin arewacin Najeriyar ne suka hallarci taron a karkashin kungiyar 'yan siyasa da ke tuntubar juna, taron da ya hada wasu daga cikin jiga-jigan 'yan siyasar yankin masu fada a ji a kasar. Wannan na cikin tarurrukan da 'yan adawar ke ci gaba da yi a kokarin kulla kawance, domin samar da babbar jam'iyyara adawa da za ta tunkari jam'iyyar APC mai mulki a kasar da a yanzu take kara cika tana tumbatsa. Jiga-jigan 'yan siyasa da suka yi takarar neman shugabancin Najeriyar wato Peter Obi na jam'iyyar Labour da Atiku Abubakar na PDP da Rotimi Amaechi tsohon minista daga yankin Kudu maso Kudancin Najeriyar, sun hallarci wannan taro ko da yake bayan da suka sa albarka a taron sun fice sun yi tafiyarsu ne.
Peter Obi da ya fito daga yanki kudu maso gabashin Najeriyar na nuna alama ta kulla kawance da yankin arewacin kasar a guguwar siyasar da ke kadawa, musamman kalaman da ya yi na cewa za a iya shawo kan matsalolin Najeriyar daga yankin arewacin. An dai fsukanci hatsaniya a wajen wannan taro daga wakilan jihar Jigawa, saboda sun turje kan wadanda aka gabatar su wakilce su. Jam'iyyun adawar sun dade suna gudanar da tarurruka a kan wannan batu na kafa babbar jamiyyar adawa, tsarin da tun daga kawancen da jam'iyyun adawar suka yi a zaben 2015 ke neman ya zama sabon yayi. A mako mai zuwa ake sa ran jam'iyyun adawar ko dai su sanar da daya daga cikin jam'iyyun SDP ko ADC, ko kuma za su yi tunanin kafa sabuwar jam'iyya.