Togo: Zargin halaka masu zanga-zanga
July 1, 2025A makon da ya gabata a Lomé babban birnin kasar Togo, dubban matasa sun fantsama a kan tituna domin yin tir da sabon kundin tsarin mulkin kasar da ya bai wa Shugaba Faure Gnassingbe ci gaba da ke rike da madafun iko. Kungiyoyin fararen hula da na kare hakkin dan Adam, sun yi ikirarin cewa an gano gawarwakin mutane bakwai a cikin kududdufai na babban birnin Togo. Sai dai fadar mulki ta Lomé ta musanta cewa tana da hannu a salwantar rayukan matasa a lokacin zanga-zangar ta kin jinin gwamnati, inda ta yi ikirarin cewa sun nitse ne a cikin ruwa. Kungiyoyi dai sun bayar da rahoton jikkatar mutane da dama yayin da aka kama "fiye da mutane 60" a cikin kwanaki uku na tayar da kayar baya, daga ranar Alhamis zuwa Asabar na makon da ya gabata.
Karin Bayani: ECOWAS tana da kalubale a gaba
A cewar mai magana da yawun kungiyar "Touche pas à ma constitution" (Kada ku taba kundin tsarin mulkina) Nathaniel Olympio abin da ya fi ci musu tuwo a kwarya shi ne, shaidun da suka ce sojojin haya na kasashen waje sun taka rawa wajen dakile zanga-zangar kin jinin gwamnatin ta Togo. Shi ma masanin kimiyyar siyasa kuma shugaban Cibiyar Nazarin Harkokin Gudanar da Mulki ta Tamberma Paul Amegakpo ya tabbatar da kasancewar sojojin haya na kasashen waje musamman daga Gambiya, wadanda suka taimakawa jami'an tsaron Togo wajen murkushe zanga-zangar adawa da tazarcen Faure Gnassingbé bayan kwaskware kundin tsarin mulkin kasar.
Sai dai gwamnatin Togo ta ce karya da kage ake yi mata saboda ba ta yi amfani da sojojin haya wajen dakile zanga-zangar kyamar mulkin gwamnatin Faure Gnassingbé ba, a cewar ministan kwadago da sasanta jama'a kuma jigo a jam'iyya UNIR (Union pour la République) mai mulki Gilbert Bawara. Kungiyar kare Hakkin dan Adam ta Kasa da kasa Amnesty International ta nunar da cewa, an ganawa wasu daga cikin masu zanga-zangar da aka kama kafin daga bisani a sake su azaba tare da wulakanta su.
Karin Bayani: Togo na sa ido a kan wayoyin 'yan adawa
Masu zanga-zangar Togo wadanda akasarinsu matasa ne, suna nuna rashin amincewarsu da kame masu sukar mahukuntan kasar tare da nuna adawa da karin farashin wutar lantarki. Kazalika, suna adawa da sake fasalin kundin tsarin mulkin kasar da ya haifar da jamhuriya ta biyar da ta bayar da damar kafa tsarin mulki da majalisar dokoki ke da karfin fada a ji, wanda Faure Gnassingbé mai shekaru 59 a duniya ya yi amfani da shi wajen ci gaba da kankane madafun ikon da ke hannunsa tun a shekara ta 2005.