Shin akwai kalubale ga APC bayan ficewar El-Rufai ?
March 10, 2025A wani sakon da ya wallafa a shafukan sa na sada zumunta tsohon gwamnan Jihar Kaduna Mallam Nasiru Elrufai ya sanar da ficewar sa daga jam'iyya APC zuwa jam'iyyar SDP mai alamar doki. Abun da ya sanya dubban‘yan sabuwar jam'iyyar da ya koma murna,abun kuma da ya janyo martani daga magoya bayan sa da sauran jam'iyyu.
Mallam Abdullahi Sani da Ibrahim Musa na daga cikin wadanda suka fito d a kafafen watsa labarai magoya bayan sa da ke numa goyan bayan su ga ficewar Elrufai sakamakon irin abubuwan da 'yan jam'iyyar ke yi masa.
Wannan mataki dai na ficewar tsohon gwamnan Kaduna ya sanya wani dan jam'iyyar da bai so a fadin sunan sa ba, cewa bai ji dadin ficewar gogan nasu ba, wanda a saboda haka ne kuma yake fargaban makomar me ka iya biyo baya. Inda kuma ya kara da cewa akwai babban hatsari da ke tattare da wannan matakin domin yin hakan zai kara janyo ra'ayin sauran ‘yan jam'iyyar APC komawa wannan sabuwar jam'iyya.