Wanne matakin tsaro China ke son kai wa?
September 3, 2025Daga cikin manyan bakin da suka halarci bikin daga kasashen 26 har da Shugaba Vladimir Putin na Rasha da Kim Jong-Un na Koriya ta Arewa, to amma kuma tuni wasu manyan kasashen duniya suka fara mayar da martani ga bikin da ke zama tamkar na gwada kwanji da Chinan ta yi. Sojoji dubu 12 ne suka gudanar da faretin a dandalin Tiananmen da ke Beijing babban birnin kasar, manyan makaman da Sin din ta baje na zamani ne kuma cike suke da siddabaru. Makaman kuma na iya dira a ko-ina cikin duniya, wanda hakan ke kara fitowa fili da kwanjin da kasar take nunawa duniya.
Karin Bayani: Amurka ta yi fito na fito da Chaina kan kudin haraji
Tsaye a dandalin na Tiananmen tamkar tsohon jagoran juyin-juya halin kasar Mao hotunan Shugaba Xi Jinping sun karade duniya, kuma cikin kasashe 26 da ke halartar kasaitaccen bikin har da na Afirka da Asiya da Amurka da ma nahiyar Turai. A bayyane take karara Chaina na son isar da muhimmin sako na sake shata tafiya, a cewar wasu masana kamar Farfesa Eberhard Sandschneider na jam'iar Berlin da ke nan Jamus. A cewar shehin malamin kuma masani kan harkokin kimiyyar siyasar kasa da kasa, tattalin arzikin Chaina da ke kara habaka a cikin hanzari karkashin jagorancin Shugaba Xi na kara ba ta kwarin gwiwa.
Sai dai kuma a cewar Kim Yong-hyun wani masani kuma malami a jami'ar Koriya ta Kudu, gayyatar shugabanni kamar Vladimir Putin na Rasha da takwaransa na Koriya ta Arewa Kim Jong-Un batu ne da ya kara tayar da kura. Mai shekaru 72 a duniya Shugaba Xi na da burin kammala daukacin tsare-tsarensa na zamani da aka dora kasar Chaina a kai shekaru 100 na kafuwarta, nan da zuwa shekara ta 2049. Abin da ka iya dora kasar kan gaba da Amurka nan da wasu shekaru masu zuwa ta fannin tattalin arziki, a cewar masana ta wannan fanni.
Karin Bayani: Sabon yakin cacar baka tsakanin Chaina da Amirka
Ko ma dai shugaban gwamnatin Jamus Fredirich Merz ya taba bayyana cewa, kasashen Asiya na kan gaba wajen bayar da misali. A yayin faretin din da ya janyo cece-kuce, an yi amfani da damar ta hanyar baje-kolin jiragen yaki da jirage marasa matuka da kuma sauran nau'ikan kayan aikin soja. A cewar Shugaba Xi a daidai lokacin da al'ummar Chaina ke zaune cikin lumana, akwai bukatar duniya ta yanke hukunci tsakanin yaki da kuma zaman lafiya. Sai dai kuma Shugaba Donald Trump na Amurka ya yi kakkausar suka game da faretin na kasar Chaina, inda ya caccaki matakin yana mai cewar yin sa tamkar yi wa Amurka makirci ne.