Kirkirarriyar basira na kara kalaman tsana a Najeriya
June 18, 2025Ci-gaban da kirkirarriyar basira da ke kawowa a harkokin yau da kullum na cike da kalubale musamman wajen aikewa da sakonnin nuna tsana da ke hadasa tashe-tashen hankula. Barnar da wannan ke yi ya dauki hankalin Majalisar Dinkin Duniya da ke aiki tare da gwamnatin Najeriya da kungiyoyin masu zaman kansu.
Karin bayani: Najeriya: Kisa ga masu kalaman batanci
Friday Odey, shugaban cibiyar kamanta gaskiya ta Najeriya ya bayyana barazanar da ke fuskantar Najeriya, inda ya ce: ‘' Wannan barazana, al'amari ne na zahiri, kuma ya riga ya iso mana. Mun ga wannan a zahiri a zaben 2023 inda aka yi amfani da kirkirarriyar basira wajen samar da bidiyo na 'yan takara. Haka wajen aikawa da sako da ke haifar da rikici a Kaduna da Filato''.
Mene ne girman wannan matsala a yanzu?
Kokarin shawo kan matsalar da kuma dakile ta ko samun raguwarta ya sanya bullo da sabbin dubaru, wacce Majalisar Dinkin Duniyar a Najeriya da hukumar kula da ci-gaban fasahar zamani ta Najeriya suka bullo da su, inda aka samar da fasahar da ke tantance irin wadannan bayanai.
Karin bayani:Batanci: Indiya na shan suka daga Musulmi
Udoka Akakem, jami'a ce a hukumar NiITDA ta bayyana cewar: ‘'Wannan manhaja na sa ido tare da tantance duk masu amfani da shafukan sada zumunta, wadanda ke aikawa da sako, wadanda suka hada da labaru na nuna kiyayya ko tsana ga wani. Ana duba dukanin bayanai da ke tada hankali da tunzura jama'a, sannan a bangare guda akwai tsarin wayar da kan jama'a."
Bukatar kara azama wajen kawar da kalaman tsana
Sai dai Dr Michael Wiener, jami'in ofishin yada bayanai na Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana abin da suke son a tabbatar wajen kauce wa take hakikin jama'a. Ya ce: ‘'Muna gani a kasashe da dama inda ake murkushe 'yan adawa da marasa karfi, a kokari na samar da kyautata lamarin, ba kawai a kan batu na ‘yanci fadin albarkacin baki ba ne, lamarin yakan wuce haka har ya kai batutuwa na jama'a su bayyana ra'ayoyinsu.''
Karin bayani:Addini: Hukuncin kisa kan matashin da ya yi batanci ga Islama
Najeriya na fatan bullo da sabbin matakai na sa ido ta yanar gizo don rage barnar da ake yi ta amfani da kirkirarriyar basira da ta zama wata sabuwar barazana da ke fuskantar duniya a yanzu.