Najeriya: Neman taimako a taron Kirisotoci
September 6, 2022Taken taron na bana dai shi ne: "Kaunar Yesu Kiristi na Zaburar Duniya Domin Yin Sulhu." Wakilai akalla 4000 daga Majami'u dabam-dabam na Cocin duniya ne suka halarci taron na kwanaki tara a birnin Karlsruhe na jahar Baden-Wutherbeg ta Jamus. DW ta tattauna da wasu daga cikinsu, shugaban Cocin Katolika reshen jihar Kaduna da ke Najeriya Reverend John Joseph Hayaf ya ce, sun halarci taron da zummar ganin manyan shugabannin kasashen duniya sun duba halin da Najeriya ke ciki na yawaitar zubar da jini da satar mutane tare da hana al'umma 'yancin gudanar da addini saboda barazanar tsaro.
Reverend Dakta Israel Akanji shugaban Kungiyar Cristian Association of Nigeria reshen jihohin da ke a tsakiyar Najeriyar, wanda shi ma ke daga cikin tawagar ya ce suna fatan ganin taron ya dauki matakin matsa wa shugabanin kasashen da ke bukatar taimako musamman ta fuskar tsaro wacce Najeriyar ta kasance a sahun gaba. Hasali ma cewa ya yi, rashin shugabancin na gari ya taka rawa wajen dagula al'amuran tsaro a Najeriya. Wannan dai ba shi ba ne karon farko da Najeriya ke mika kokon bararta ga babban taro irin wannan ba, kafin rikicin Boko Haram ya yi kamari ma ta taba kawo kuka gaban wannan taro. Sai dai har kawo yanzu ta tabbata cewa ba ta sauya zani ba, Reverend Akanji ya ce akwai matakan da shugabannin duniya za su iya dauka da kuma za su iya yin tasiri wajen shawo kan matsalolin.