Kiristocin duniya na gudanar da bukukuwan Easter
April 18, 2025Talla
Mabiya addinin Kirista na yin bikin ne don tunawa da mutuwa da tashin Isa Almasihu, wanda suka yi imani ya mutu ne don ceton bil’Adama daga shiga jahannama, matukar sun yi imani da farillansa.
Lokacin bikin dai masu bin Yesu Almasihu za su sadaukar da kai wajen yin rayuwa da ta dace da yin addu’o’i na samar da zaman lafiya. A kasar Ghana da wasu sauran kasashe irin su Najeriya da Nijar yanzu haka mabiya addinin Kiristan sun soma gudanar da bukukuwan na Easter.