SiyasaYuganda
Jagoran adawar Yuganda ya gurfana a kotu
May 21, 2025Talla
A daidai lokacin da jagoran adawar kasar Yuganda Kizza Besigye ya gurfana a gaban kuliya domin sauraron karar da ake masa ne, Kenyan ta amince tana da hannu dumu-dumu a sace shin da aka yi. An dai sace Besigye mai shekaru 68 a duniya a Nairobi babban birnin kasar Kenya a watan Nuwambar bara, kana kwanaki kalilan bayan sace shi ya bayyana a kotun sojoji a Yuganda. Besigye dai na zaman tsohon likitan Shugaba Yoweri Museveni na Yuganda da ke mulkin kasar na kusan tsawon shekaru 40, kafin daga bisani ya juya masa baya.