Kazakhstan ta ki ba da kofar bincike
January 29, 2022Wasu jami'an Kazakhstan da Shugaba Tokayev sun daura alahakin rikicin da ya jefa kasar mai arziki a cikin tashin hankali a farkon shekarar 2022 kan 'yan bindiga da 'yan ta'adda da ke samun tallafin kasashen waje. Sai dai babu hujjojin da kasar ta gabatar da zai iya kare wannan zargi.
A cikin hirarsa ta farko da aka watsa a gidan talabijin tun bayan barkewar rikicin, Tokayev ya sake nanata cewa Kazakhstan na fuskantar hare-hare daga masu fafutuka, kuma ya jaddada aniyar kasar na yin bincike ba tare da taimakon kasashen waje ba.
Kungiyoyin kare hakkin bil Adama da Majalisar Tarayyar Turai na daga cikin wadanda suka matsa kaimi wajen gudanar da bincike na kasa da kasa kan tashin hankalin da ya barke bayan zanga-zangar lumana da aka yi tun farko da ta shafi tashin farashin mai a yammacin kasar, kafin a kai ga wasu bukatun siyasa.