An fa kai kayan agaji zirin Gaza
May 19, 2025Firaminista Benjamin Netanyahu na Isra'ila ya bayyana cewa matakin kawo karshen dillace yankin zirin Gaza na Falasdinu na watanni biyu da rabi na da nasaba da matsin lamba daga kasashen da suke dasawa da kasarsa. Isra'ila ta ce manyan motoci biyar shake da kayan agaji na Majalisar Dinkin Duniya suka shiga yankin na zirin Gaza.
Karin Bayani: Hamas ta sako dan Amurka da ta tsare a Gaza
Firaministan ya ce kasarsa za ta karbe iko da daukacin yankin zirin Gaza na Falasdinu. Dillace yankin na Zirin Gaza da dakarun Isra'ila suka yi, ya haifar da matsalolin jinkai, a baya dai an samu kwarya-kwaryar yarjejeniyar tsagaita wuta ta tsawon watanni biyu. Wannan yankin na zirin Gaza yana dauke da mazauna kimanin milyan 2.3.
Tun ranar Jumma'a sojojin Isra'ila suka bayyana sabon farmaki tare da gargadin mazauna yankin.