Yaushe za a dakile matsalar tsaro a Katsina?
August 8, 2025Wannan dai shine karon farko da gwamnatin jihar Katsina ta shirya irin wannan taron na bai wa al'umma maza da mata da matasa damar su bayyana ra'ayoyinsu da bukatunsu. Duk da cewa gwamnatin jihar ta bayar da damar jin ra'ayoyin al'ummar ne kan bukatunsu da za ta mayar da hankali a kasafin kudin shekara mai zuwa musamman abin da ya shafi ayyukan raya kasa, sai dai da dama sunce matsalar tsaro ita ke a gabansu.
Suma mata a nasu bangaren sun nemi daukin gwamnatin jihar musamman yadda sukace matsalar tsaro ta lakume rayukan mazajensu an barsu da yara, dangane da haka burinsu shi ne samun sana'a. Sai dai gwamnatin jihar ta ce bikin Magaji ba ya hana na Magajiya, kuma da ma matsalar tsaro tuni ta tunkare ta haikan. Gwamnatocin jahohin arewacin Najeriya na ci gaba da kokarin magance matsalar tsaro da ta addabe su, abin da ya sa yanzu ake kokarin yin sulhu da 'yan bindiga. Koda yake wasu na ganin shirirtace kawai, saboda an dade ana sulhun amma maharan na tuban mazuru.