SiyasaGabas ta Tsakiya
Iran ta harba makamai Katar da Iraki
June 23, 2025Talla
Kasar Iran ta kaddamar da hare-haren makamai masu linzami kan sansanonin sojan Amurka da ke Katar da Iraki, a matsayin martani na hare-haren Amurka kan tashoshin nukiliyar kasar ta Iran, abin da ke kara zaman zullumi a rikicin da ke kara rancabewa a yankin Gabas ta Tsakiya.
Karin Bayani: Wane mataki kawayent Iran za su iya dauka wajen taimaka mata?
Kafofin yada labaran Iran sun ce an kai hare-haren kan sansanin sojan Al Udeid da ke kasar Katar. Tuni kasar Katar ta yi tir da wannan hare-haren da kasar Iran ta kaddamar.
Tun farko Isra'ila ta bayyana cewa cikin kankanin lokaci za ta kawo karshen hare-haren da ta kaddamar kan tashoshin nukiliyar Iran. Tun lokacin da Isra'ila ta kaddamar da hare-haren ake fito na fito tsakanin bangarorin biyu.