China za ta sanya harajin kishi 34 kan Amurka
April 4, 2025Kasuwannin hannayen jari na Turai sun fadi warwas a yau jumaa bayan da China ta mayar da martani ga karin harajin Amurka,
lamarin da ya kara dagula fargabar karuwar tashe-tashen hankulan kasuwanci tsakanin manyan kasashe biyu mafi karfin tattalin arziki
Kasuwar hanayen Jari ta CAC 40 dake a birnin Paris ta fadi da kashi 4.26%, wadda ita ce faduwa mafi muni da ta yi tun a cikin watan Maris na shekara ta 2022.
Frankfurt da London sun fadi da kashi 4.95%, Milan da kashi 6.53%, faduwa mafi girma tun farkon barkewar cutar Corona a cikin watan Maris na shekara ta 2020
Gwamnatin kasar China ta sanar da cewar, za ta sanya harajin kashi 34 cikin 100 kan dukkanin kayayyakin da ake shigo da su daga Amurka daga ranar 10 ga watan Afrilu, a matsayin martani ga sabbin harajin da Amurka ta kakaba kan kayayyakin kasar Chinar.