Kasashen Turai za su tattauna makomar Ukraine
February 16, 2025Shugabannin kasashen Turai za su tattauna a Paris a ranar Litinin kan batun shirye-shiryen shugaban Amurka Donald Trump na kawo karshen yakin Ukraine.
Firaministan Faransa Jean-Noël Barrot ne ya tabbatar da batun tattaunawar a wata hira da ya yi da kafar yada labarai ta France Inter a ranar Lahadi.
Zelensky ya gana a karon farko da JD Vance kan yakin Ukraine da Rasha
Ko da yake Barrot bai fadi sunayen shugabannin da za su halarci taron ba, amma ya ce shugaban Faransa Emmanuel Macron ne zai jagorance shi.
Masana diflomasiyya na cewa taron zai mayar da hankali ne kan yadda kasashen Turai za su taimaka a samu yarjejeniyar zaman lafiya a Ukraine mai fama da yaki.
Burtaniya ta bukaci Turai ta taka rawar gani a kungiyar tsaro ta NATO
Tun bayan tattaunawar wayar tarho da shugaban Amurka Donald Trump ya yi da takwaransa na Rasha Vladimir Putin ne ake nuna damuwa a Turai kan wata kila ayi babu su a kokarin cimma yarjejeniyar zaman lafiya.