SiyasaAsiya
Kasashen Turai na matsin lamba ga Amurka kan tsaron Ukraine
August 17, 2025Talla
Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya ce shugabannin kasashen Turai za su bi diddigin tabbacin tsaro da shugaban Amurka zai tabbatarwa da Ukraine, duk da cewa basu da yakinin Rasha za ta amince da daftarin wanzar da zaman lafiya.
Karin bayani:Ganawar Trump da Putin a kan yakin Ukraine
Macron ya sanar da hakan a wajen shakatawar shugaban kasa gabanin taron da shugabannin kasashen Turai da za su yi da takwaransu na Amurka domin sake jaddada goyon baya ga shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky a ganawarsa da Donald Trump.