Kasashen OIC sun goyi bayan Masar kan gina Gaza
March 8, 2025Kasashen Larabawa na ci gaba da samun goyon baya a kudurin da suka amince da shi wanda Masar ta gabatar kan sa ke gina Zirin Gaza.
Kudurin na Alqahira ya yi hannun riga da bukatar shugaban Amurka Donald Trump ta karbe iko da zirin tare da mayar da shi wani wurin shakatawa.
Trump ya ba da shawarar Amurka ta mallaki zirin Gaza
Bayan baki daya da kasashen na Larabawa suka yi, suma wasu na Turai da na Musulmi a fadin duniya sun amince da kudurin.
Burtaniya da Faransa da Italiya da kuma Jamus duk sun goyi bayan shawarar ta kasashen Larabawa baya ga kungiyar kasashen Musulmi mai mabobi 57.
Ministan harkokin wajen Saudiyya Yarima Faisal bin Farhan, ya isa Masar kan sake gina Falasdinu
Kudurin na Masar kan sake gina Gaza ya bukaci a gina zirin ba tare da daidaita Falasdinawa sama da miliyan 2.4 ba.