Kudirin Trump kan Gaza na shan adawa
February 19, 2025Kamfanin dillancin labaran kasar ta Hadaddiyar Daular Larabawa WAM ne ya ruwaito hakan, inda ya ce kalaman na Shugaba Sheikh Mohammed bin Zayed na zuwa ne sakamakon kudurin shugaban Amurka Donald Trump na kwace iko da yankin Zirin Gaza na Falasdinu tare da raba mazauna yankin zuwa kasashe makwabta.
Al Nahyan ya bayyanawa sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio da ke ziyara a yanzu haka a birnin Abu Dhabi bayan kai ziyara a Isra'ila da Saudiyya cewa, yana da muhimmanci a alakanta gyaran yankin na Zirin Gaza da matakin kawo karshen rikicin Isra'ila da Falasdinu na din-din-din ta hanyar samar da kasashe biyu.
Matakin na Hadaddiyar Daular Larabawa kan wannan rikici na da matukar muhimmanci, kasancewarta guda cikin Kasashen Larabawa hudu da suka kulla kawance da Isra'ila a lokacin mulkin Trump na farko da kuma yadda ta taka rawa wajen sake gina Gazan a lokutan baya.